An zargi wasu Jami'an FIFA da karbar hanci

Jamian FIFA

Ana zargin jami'ai 3 na kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA, wadanda ke cikin masu jefa kuri'ar wanda zai dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara ta 2018 da 2022 da karbar cin hanci domin samar da kwangiloli masu tsoka ga kamfanoni.

Wani shiri na musamman na gidan talabijin na BBC na Panorama, ya bankado cewa Ricardo Teixeira na kasar Brazil, Nicolas Leoz na Paraguay da Issa Hayatou na Kamaru sun karbi makudan kudade daga wani kamfanin saida kayayyikin wasanni a shekarun 1990.

Shirin na Panorama yace an yi tonan sililin ne kasa da kwanaki kadan gabanin yanke shawarar kasar da zata dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta shekara ta 2018.

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta FIFA dai ta ki yadda a yi hira da jami'anta a cikin shirin na Panorama.