An kashe wani masanin kimiyyar nuclear Iran

shugaba Ahmadinedjad na Iran
Image caption An kashe wani masanin kimiyyar nuclea a Iran

Kafofin yada labarai a Iran sun ce an kashe wani masanin kimiyyar nukilya na kasar kuma an jikkata wani, a wasu hare-haren bam guda biyu da aka kai a Tehran, babban birnin kasar.

Mutumen da aka hallaka, Majid Shahriari, yana tuka motarsa zuwa wurin aiki ne, lokacin da maharan da ke kan babura suka dana bam a jikin motar tasa, suka kuma tsere.

Daya masanin kimiyyar da ya jikkata sosai, Fereidoun Abbasi, shi ma irin wannan harin ne aka kai masa.

Gwamnatin Iran ta dora alhakin hare-haren a kan hukumomin leken asirin Amirka da na Isra'ila.