Majalisar dokoki za ta yi zaman sauraron bahasi

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption Majalisar zata saurari bahasi kan kudurin doka

A Najeriya, a yau ne majalisar dokokin kasar za ta yi zaman jin bahasi kan kudirin dokar dake neman baiwa 'yan majalisar wakilci a kwamitocin zartarwar jam'iyyunsu.

Shi dai wannan kuduri mai cike da kace-nace ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilan kasar.

Sai dai a hirarsa da BBC, Mohammed Ali Ndume, dan majalisar wakilai ya ce, za su amince da kudirin dokar ne domin tabbatar da adalci a cikin jam'iyyu.

Ya ce: ''Mu('yan majalisa), muna ganin ba za a taba samun ingantaccen zabe a kasa ba, idan ba a samu ingantaccen zabe a cikin jam'iyu ba''.

Sai dai ya kara da cewa, zaman sauraron bahasin zai baiwa jama'a damar bayyana ra'ayinsu kan kudurin dokar ne, kuma idan jama'a basu amince da shi ba, majalisa ba zata zartar da shi ba.