Amurka na kokarin rage illar fallasar Wikileaks

Hilary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta kwatanta fallasa dubban bayanan sirrin da Wikileaks yayi, a matsayin wani hari ba wai kan Amurka kadai ba, a'a har ma da sauran kashen duniya baki daya.

Mrs Clinton tace ta yi imanin wannan lamari ba zai lalata dangantakar tsakanin Amurka da kuma sauran kasashen duniya ba.

Tuni dai ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka ta bada umurnin a sake yin nazari akan yadda bayanan sirri ke fitowa.

Yayin da shi kuma Antoni janar na Amurkar Eric Holder ya ce za a gudanar da bincike, kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi.

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad ya yi watsi da bayanan da shafin na Wikileaks ya wallafa yana mai cewa shirme ne kawai, kuma ba zai shafi dangantakar su da makwabtanta kasashen larabawa ba.