China na son a hade kasashen Korea

Taswirar kasar China
Image caption China na son a hade kasashen Korea

Daya daga cikin sakonnin da shafin kwarmata bayanan sirri a intanet wato Wikileaks ya wallafa, ya nuna cewa China za ta iya goyon bayan hadewar kasar Koriya ta kudu da ta arewa zuwa kasa daya.

Shafin ya ce wasu manyan jami'an Chinan guda biyu na shaidawa takwarorinsu na Koriya ta kudu cewa, babu wani alfanu da Koriya ta arewa ke tsinana mata, kuma Chinan za ta goyi bayan sake hadewar kasar karkashin ikon Koriya ta kudu.

Wikileaks ya ce jami'an sun yi tattaunawar cikin sirri ne, inda daga bisani daya daga cikinsu ya shaidawa jakadar Amurka a kasar, Kathlen Stephen abin da tattaunawar ta kunsa.

Sakon ya kuma nuna cewa China ta goyi bayan matakin ne da sharadin cewa sabuwar kasar ba za ta yi adawa da ita ba.