Yaki da damfara ta hanyar intanet a yammacin Afirka

Shafin intanet
Image caption Shafin intanet

A Najeriya an bude taron koli, a kan batun yaki da matsalar damfara da sauran laifufuka ta hanyar sadarwar intanet a Afirka ta yamma.

Taron na kwanaki biyar, na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriyar ta'annati, EFCC, da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, da kuma kamfanin Microsoft.

Hukumar EFCC ta ce ta shirya taron ne, da nufin hada karfi da karfe don yaki da aikata laifuka ta intanet.

Kididdiga ta nuna cewa, a bara wasu kasashen yammacin Afirka suna cikin jerin kasashen duniya goma, inda aka fi aikata laifufuka ta intanet.