EFCC ta na yiwa Babban Manajan Kamfanin Shell tambayoyi

Kamfanin Mai

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa a Nigeria, watau EFCC na yiwa jami'an wasu kamfanoni tambayoyi dangane da batun cin hanci da rashawa.

Kamfanonin da lamarin ya shafa sun hada da kamfanin Hallibortun, da kamfanin mai na Shell da kuma kamfanin mai na Panalpina.

Hukumar ta ce ta na yiwa Babban Jami'in kamfanin Halliburton tambaya ne akan abun kunyar nan na cin hanci da rashawa da ya tassama dola miliyan 180 da ake zargin an baiwa wasu jami'an Nigeria.

Kamar yadda kakakin hukumar, Mr Femi Babafemi, ya bayyana an gayyaci kamfanin Shell ne dangane da wani zargin bayar da cin hanci da rashawa daban na dola miliyan 240.

Dukkan wadannan kamfanoni dai sun biya tarar miliyoyin daloli a Amurka dangane da batutuwan da hukumar ta EFCC take bincike akai.