Matsanancin Halin Rayuwa: Muhalli

Wannan zagaye na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa zai duba al'amuran muhalli.

A shekarun baya-bayan nan 'yan siyasa a duniya na fadi-tashin shawo kan matsalar sauyin yanayi da kuma gurbatar muhalli.

Wani rahoto na hukumar Kare Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai banbanci mai yawa tsakanin abinda masana kimiyya ke fada da kuma abinda 'yan siyasa ke aikatawa.

Matsalar tattalin arziki ta sa adadin gurbatacciyar iskar da ake fitarwa ta ragu amma da kashi 1 da digo 3 kacal a shekara ta 2009.

Alkaluman da Hukumar Makamashi ta Duniya ta fitar sun nuna cewa kasashen Amurka da China ne suka fi fitar da iska mai gurbata muhalli.