Matsanancin Halin Rayuwa: Miyagun laifuka

Kashi na biyar na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa zai duba mayagun laifuka a duniya

Kusan mutane miliyan goma ne ke tsare a gidajen yari daban-daban a duniya. Kusan rabi ana tsare da su ne a Amurka da China da Rasha.

Adadin 'yan gidan yari na duniya a bara ya nuna cewa Amurka na daure mutane 756 a cikin kowanne mutane dubu 100. Yayin da a duniya adadin ya tsaya a mutane 145 cikin mutane dubu 100.

A bangare guda kuma, kasar Liechtsenstein na da fursunoni bakwai kacal a shekarar 2008 - duk da cewa ana tsare da wasu daga cikin fursunoninta a kasar Australia. Mutane 20 ne kawai ke zaman gidan yari a cikin dubu 100 a kasar.

Kasashen tsakiya da kuma Kudancin Amurka, a nan ne aka fi aikata laifukan kisan gilla da kuma yanka mutane a duniya.