Matsanancin Halin Rayuwa: Tsananin sanyi

Matsanancin Rayuwa
Image caption Shrin Matsanancin Halin Rayuwa na BBC

Matsanancin Halin Rayuwa wani sabon shiri ne da za a watsa ta gidan rediyo da talabijin da kuma intanet, wanda zai duba banbance-banbancen da ke tsakanin mu.

Nan da 'yan watanni masu zuwa, wakilan BBC za su yi karin haske kan wasu a abubuwa masu mahimmanci, wadanda suka hada da yadda yara ke samun ilimi da kuma yadda ake shawo kan miyagun laifuka a sassa da daban-daban na duniya.

Yanayin sanyi mafi muni da a ka taba fuskanta a duniya shi ne na -89 da digo biyu a tashar Vostok da ke Antarctica a ranar 21 ga watan Yulin 1983. Wurin da ake tunanin ya fi kowanne zafi a duniya shi ne wani dan karamin tsibiri na Dallol da ke kasar Habasha - inda yanayin yake kasancewa a ma'aunin salshiyos 34 a shekarar baki daya.

Sai dai rahotanin baya-bayan nan sun nuna cewa a yanzu babu wasu mutane da ke zaune a wannan garin na Dallol.