Matsanancin Halin Rayuwa: Zai bayyana bambancin rayuwa a sassan duniya

Matsanancin Yanayin Rayuwa wani sabon shiri ne da za'a watsa ta gidan rediyo da talabijin da kuma intanet na BBC, wanda zai duba banbance-banbancen da ke tsakanin al'umma.

Nan da 'yan watanni masu zuwa, wakilan BBC za su yi karin haske kan wasu abubuwa takwas da suka banbanta yadda muke rayuwa.

A shirin farko, wanda zai duba yanayin zafi da sanyi, wakilin BBC Adam Mynott zai ziyarci kauyen Oymyakon na kasar Rasha, inda aka ce shi ne yafi kowanne yanki tsananin sanyi a duniya.

A garin Omyakon, matsakaicin yanayi a watan Janairu shi ne -46 digiri a ma'aunin salshiyos. Shi dai yankin na da arzikin gwal da kuma daiman - kuma a yanzu Rasha na daya daga cikin kasashen da suka fi samar da daiman a duniya.