Masu sa ido sun gamsu da zaben Haiti

Ma'aikatan zabe a kasar haiti
Image caption Masu sa ido sun gamsu da zaben da aka yi a Haiti

Masu sa ido na kasa- da-kasa kan yadda aka gudanar da zabe a Haiti, sun bayyana gamsuwa da sahihancinsa duk da kurakuran da suka ce an tafka.

Jagoran masu sa ido daga kungiyar kasashen nahiyar Amurka da Carribean, Colin Granderson, ya ce jinkirin da aka samu a wasu rumfunan kada kuri'a bai isa hujjar a soke zaben ba.

Ya ce:''Bayan nazari akan yankunan zabe goma sha daya, tawagar ta mu ba ta ganin wadannan kura-kurai duk da girman wasu daga cikinsu, sun isa su rushe ingancin zaben''.

Mafi yawan 'yan takarar jam'iyyun adawa dai sun bukaci a soke zaben bisa zargin gwamnatin Haiti ta tafka magudi.