Yajin aikin direbobin tankoki ya fara tasiri

Matsalar Mai a Nigeria

A Nigeria, yanzu haka yajin aikinda kungiyar direbobi masu dakon man fetur ta shiga ya fara haifar da matsalar Man Fetur a wasu sassa na kasar.

Tuni aka fara samun dogayan layuka a manya manyan birane na kasar da suka hada da Lagos da Kaduna da kuma Kano.

Kungiyar direbobin tankokin Man ta shiga yajin aiki ne a farkon wannan makon, inda take so a gurfanar da wasu sojoji da kungiyar ta ce suna hallaka 'ya'yanta da kuma yin garkuwa da manyan motocinsu akan hanyoyin kasar.

Masu aiko da rahotanni sun ce tuni, jamaa sun fara dandana kudarsu a sakamakon wannan yajin aiki.

Ana sa ran gwamnati zata gana tare da shugabannin kungiyoyin anan gaba a yau domin warware matsalar.