Ranar tunawa da masu AIDS

Ranar yaki da AIDS
Image caption Ranar yaki da AIDS

Yau ce ranar yaki da cutar AIDS ko SIDA, mai karya garkuwar jikin dan adam.

An gudanar da bukukuwa a sassa dabam dabam na duniya, domin fadakar da jama'a a kan cutar - yadda za su kare kansu daga kamuwa da ita, da irin kulawar da masu dauke da cutar zasu iya samu a cibiyoyin lafiya, da kuma yadda sauran jama'a za su iya kula da su, ko kuma tausaya masu.

Hukumar yaki da cutar a Ghana ta ce mutane sama da dubu 120 ne ke dauke da cutar a kasar.

A Nijar masu fama da SIDA sun yi kira ga hukumomin kasar da su kara tashi tsaye, wajen daukar dawainiyar masu fama da cutar, ta hanyar kara yawan asibitoci da kwararrun likitoci.

Tun daga ranar 1 ga watan Disamban 1988 ne ake bukukuwan tunawa da masu fama da cutar AIDS a duniya.

A yanzu haka fiye da mutane miliyan 33 ne a dukan fadin duniya ke dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa SIDA, da kuma cutar kanta.