Akwai yiwuwar Koriya ta Arewa ta kara kai hari

Sojin koriya ta Kudu
Image caption Akwai dadaddiyar damuwa a yankin Koriya

An rawaito babban jami'in tsaro na Koriya ta Kudu ya ce akwai yiwuwar Koriya ta Arewa ta kara kai hari, mako guda bayan wanda ta kai a tsibirin Koriya ta Kudu.

Kalaman na sa sun zo ne sa'o'i kadan bayanda jami'ai suka ce Koriya ta Kudu da Amurka na shirin sake gudanar da atisayin soji.

A ranar 23 ga watan Nuwamba Koriya ta Arewa ta kai hari da makamai masu linzami a tsibirin Yeonpyeong, inda ta kashe a kalla 'yan kasar Koriya ta kudu hudu.

An dade ana fama da tashin hankali a kan iyakokin kasashen biyu, wadanda ba sa, ga muciji da juna.