Gwamnan CBN a majalisar dokokin Najeriya

Gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta gayyaci gwamnan babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi, da kuma ministan kudi Olusegun Aganga, domin amsa tambayoyi a kan sanarwar da suka yi, dangane da kudaden da ake kashewa majalisar dokokin kasar.

Majalisar ta kuma gayyaci Hajiyar Amina Ibrahim, shugabar shirin nan na cimma muradun ci gaba na karni, wato MDGs, domin ta yi bayyani akan yadda ake kashe kudaden da ake warewa 'yan majalisar, domin gudanar da ayyukan cigaba a mazabunsu.

A karshen makon da ya wuce ne gwamnan babban bankin yayi zargin cewa, ana kashe kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin Najeriyar a kan majalisar dokokin, kuma gwamnati na duba yiwuwar zabtare kudaden.

'Yan majalisar dai sun fusata sosai da wannan zargi, kuma hakan yana iya haifar da rashin jituwa tsakanin bangaren majalisar da kuma na zartaswa.