Majalisar shari'ar Musulunci ta koka a kan Boko Haram

Tutar najeriya
Image caption Majalisa tana ganin ya kamata a yafe wa 'yan Boko Haram

Majalisar koli ta shariar musulunci a Najeriya, ta nuna damuwa bisa abinda ta ce barazanar da ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram suka fara yi wa yayanta.

Majalisar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Kaduna, inda ta ce alamu sun nuna cewa wasu daga cikin malaman da ke majaisar na fuskantar barazana a bisa rayukansu da na iyalansu daga kungiyar ta Boko Haram.

Duk dai da wannan fargaba, majalisar na ganin ya kamata gwamnati ta duba batun yi musu afuwa kamar yadda ta yi wa ‘yan gwagwarmayar yankin Naija Delta.