An sabunta: 1 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 12:57 GMT

Ra'ayi Riga: Matsalolin tsaro a lokutan zabe a Najeriya

Matsalolin tsaro a lokutan zabe a Najeriya

An dade ana nuna shakku kan rawar jami'an tsaron kasar a lokutan zabe

A yayin da zabukan Najeriya ke kara karatowa, wani batu da ke damun yawancin 'yan kasar shi ne na matsalar tsaro a lokacin zabe.

Wani abin damuwa kuma shi ne yadda hukumomin tsaro suka kama makamai a gabar ruwan Legas, wanda wasu ke ganin ba zai rasa nasaba da yadda wasu ke daukar zabukan na badi ba, na ko a mutu ko ayi rai.

Shin ta yaya za a iya kaucewa matsalar tsaro a lokutan zabe a Najeriya?

Ko a kwai wata rawa da 'yan Najeriya za su iya takawa domin kaucewa fadawa rikicin zabe?

Wadannan na daga cikin abubuwan da za mu tattauna a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako:

Domin shiga cikin shirin sai ku aiko mana da takaitattun ra'ayoyinku ta adreshinmu na email, wato hausa@bbc.co.uk, ko ta lamba 447786202009 ko kuma ta dandalin mu na muhawara, BBCHausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na internet, wato bbchausa.com

Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbi:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.