Bayanan Wikileaks dangane da makaman nukiliyar Pakistan

Shafin Wikileaks
Image caption Bayanan da wikileaks ya fitar na nuni da cewar kasashen Amurka da Burtaniya da Rasha sun damu matuka game da tsaron makaman nukiliyar kasar Pakistan

Wasu takardu na baya bayan da shafin Internet na Wikileaks ya fitar sun nuna cewa kasashen Burtaniya, da Rasha da Amurka dukkaninsu sun nuna damuwa game da tsaron makaman nukiliyan kasar Pakistan.

A bara rahotanni sun ambato Jakadan Amurka a Islamabad, Anne Patterson, na cewa babban abin damuwa shine, wasu ma'aikata a kasar ta Pakistan ka iya cire wasu kayayyakin kera makaman nukiliya da zai basu damar harhada wasu makaman nukiliya nasu na kashin kansu.

Jami'an kasar Pakistan din dai sun tabbatar da tsaron kayayyakin kera makaman nukiliyar kasar

A wata takardar kuma shugaba Obama na Amurka ya bayyana Pakistan a matsayin kasar dake hana shi sukuni.