An tura karin dakaru zuwa kasar Congo

Jamhuriyar dumukradiyyar Congo
Image caption Majalisar dinkin duniya ta tura karin dakarunta zuwa jamhuriyar dumukradiyyar Congo don kaucewa hare haren 'yan tawaye

Majalisar Dinkin Duniya ta kara yawan dakarunta na wanzar da zaman lafiya a gabashin Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo don kaucewa kai hare hare daga kungiyar 'yan tawayen nan ta Lord's Resistance Army, gabannin bukukuwan kirsimeti.

Kakakin rundunar Laftanar kanar Amadou Gaye, ya shaidawa BBC cewa an kara yawan dakarun ne don kaucewa abkuwar irin abubuwan da suka faru shekaru biyun da suka gabata, inda kungiyar 'yan tawayen suka kashe kimanin mutane dari biyu.

Kanar Gaye ya ce wannan aikin ya hada da kafa wasu sansanonin soji da kuma tsaurara matakan tsaro don hana kaiwa fararen hula hare hare.