FA za ta binciki Birmingham da Aston Villa

Birmingham da Aston Villa
Image caption Wannan nasara ta baiwa Birmingham damar zuwa wasan kusa da na karshe

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila za ta gudanar da bincike kan hargitsin da ya biyo bayan nasarar da Birmingham ta samu a kan Aston Villa da ci 2-1 a gasar cin kofin Carling.

Daruruwan magoya bayan Birmingham ne suka afkawa na Villa, kuma akai ta jefe-jefe a filin wasan na St Andrew.

"Mun yi Allah wadai da duk wanda ke da hannu a wannan tashin hankali," a sanarwar da FA ta fitar.

FA ta nemi duka kungiyoyin biyu da su dauki matakai masu tsauri kan magoya bayansu, ciki har da dakatarwa.

Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da ake shirin kada kuri'a domin neman kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Abin da masana ke ganin zai iya kunya ta Ingila a kokarinta na shawo kan masu kada kuri'a domin su zabe ta.