Alassane Ouattara ya lashe zaben Ivory Coast

Alassane Ouattara da Laurent Gbabo
Image caption Alassane Ouattara ya lashe zaben shugaban kasar Ivory Coast

Shugaban hukumar zaben kasar Ivory Coast ya bayyana jagoran yan adawa Alassane a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Ya lashe zaben ne da kashi hamsin da hudu cikin dari na kuriunda aka kada a zagaye na biyu na zaben, yayinda shugaban kasar mai ci Laurent Gbagbo ya samu kashi arbain da biyar da digo tara cikin dari.

A bangarori da dama a birnin Abidjan, magoya bayan Quattara sun yi ta yin tururuwa a kan tituna domin nuna farin cikinsu.

Akwai alamar cewa majalisar tsarin mulkin kasar za ta kalubalanci zaben, wadda ita ce ke da alhakin amincewa da sakamakon zaben.