An kai hari kan 'yan adawa a Ivory Coast

Ivory Coast
Image caption Wannan ne karo na farko da ake zabe a kasar cikin shekaru goma

An kai hari kan ofishin jagoran 'yan adawar kasar Ivory Coast Alassane Ouattara, inda wasu rahotanni ke cewa an kashe mutane da dama.

Tashin hankalin ya barke ne duk da dokar hana yawon daren da aka sa, a daidai lokacin da aka debarwa hukumar zaben ta bayyana sakamakon ke wucewa.

Magoya Shugaba Laurent Gbagbo na hada bayyanan sakamakon zaben, suna mai cewa an tafka magudi a yankin Arewacin kasar, inda mista Ouattara ke da farin jini.

Wannan ne zabe na farko da aka gudanar a kasar cikin shekaru goma.

Tashin hankali a shekara ta 2002 ya raba kasar gida biyu tsakanin masu goyon bayan gwamnati da kuma 'yan tawaye.