JTF ta kai hari sansanonin masu gwagwarmaya

Masu gwagwarmaya
Image caption Masu gwagwarmaya a Niger Delta

Rundunar Jami'an tsaro ta hadin guiwa da ke kula da tsaro a yankin Niger Delta ta kai wani samame zuwa wasu sansanonin masu gwagwarmaya ukku a yankin Niger Delta.

Hukumar ta ce ta samu gagarumar nasara a samamen da ta kai, in da ta ce ta kama manya manyan makamai.

Rundunar jami'an tsaron ta bayyana cewa ta kai farmakin ne a wasu sansanonin uku dake kusa da garuruwan Ayakoroma da okrika da ke jihar Delta.

Wani babban jami'in rundunar sojojin Nigeria ya ce an kai harin ne wasu sansanoni da ke karkashin ikon John Togo.

Ana zargin John Togo da wasu aikace aikacen da suka ha da fashi da makami da fyade da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudi a Jihar Delta.