Kankara ta hana zirga-zirga a wasu sassan Burtaniya

Kankara ta hana ziraga-zirga a wasu sassan Burtaniya
Image caption Abin dai ya shafi sassa da dama na kasar

Matafiya na ci gaba da fuskantar kalubale a wasu sassa da dama na Burtaniya, bayanda kankara ta toshe filayen jiragen sama da hanyoyin mota da tashoshin jiragen kasa.

An kara adadin sa'o'in da aka rufe filin saukar jiragen sama na Gatwick zuwa karfe shida na ranar Juma'a, bayan karuwar kankarar da ke zuba.

Kamfanin jiragen kasa na Southern ya dakatar da zirga-zirga yayin da na Southeastern ke yin ayyukan gaggawa kawai.

Mahukunta sun yi gargadin zubar kankara mai yawan gaske a yankin Scotland da kuma Kudanci da Gabashin Ingila. A kalla makarantu 6,500 aka rufe a fadin Burtaniya.

Sakataren sufuri Philip Hammond, ya ce an fara bincike kan yadda kamfanonin sufuri suka tunkari yanayin da kasar ta samu kanta.