Obama ya kai ziyara Afghanistan

Shugaba Obama yayi gargadin cewa akwai jan aiki a gaba a Afghanistan, duk kuwa da ci gaban da aka samu a yakin da ake da 'yan Taliban.

Mr Obama na jawabi ne ga dakarun Amurka a lokacin wata ziyarar ba-zata zuwa Afghanistan.

An shirya kuma zai gana da shugaba Hamid Karzai, amma fadar White House ta ce sun yi magana ta waya, a sakamakon rashin kyaun yanayi, da ya hana shugaba Obama zuwa birnin Kabul.

Ziyarar ta zo ne yayinda fadar White House ke shirin fito da nazarin manufofinta a Afghanistan, bayan kara yawan sojojin Amurka a a can shekara guda da ya wuce. .