Yau ce ranar nakasassu ta duniya

Ranar nakasassu ta duniya
Image caption Yau ake bukin tunawa da ranar nakasassu ta duniya, ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin duba halin da nakasassun ke ciki

Yau ne dai ake bukin tunawa da ranar nakasassu ta duniya, ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin duba halin da nakasassun ke ciki tare da kokarin jan hankulan hukumomi game da muhimmacin bayar da cikakkiyar dama da 'yanci ga nakasassun ta fannonin zamantakewa, da siyasa, da tattalin arziki da sauran abubuwan da suka shafi ci gaban rayuwar su.

A Najeriya, babban kalubalen da nakasassun ke fuskanta dai shine yadda mafi yawan jama'a ke musu kallon mabarata, koda yake, hakan bai rasa nasaba da yadda wasunsu suka zabi hanyoyin yin bara ba, ko da kuwa zasu iya yin wasu sana'o'i.

A Jamhuriyar Kamaru ma nakasassu zasu bi takwarorinsu na sauran kasashen duniya don gudanar da bukin tunawa da ranar da aka ware musu.

Duk da cewa Gwamantin kasar tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suna kokarin ganin halin rayuwar nakasassun kasar ta kyautatu, wasu na ganin akwai sauran aiki a gaba don ganin masu fama da nakassa sun fita cikin kangin da suke ciki.