Andy Anson ya nemi a sauya tsarin FIFA

Shugaban FIFA yana sanar da kasar da ta yi nasara
Image caption Shugaban FIFA Sepp Blatter yana sanar da kasar da ta yi nasara

Jagoran tawagar da ta nemar wa Ingila gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 Andy Anson, ya gargadi kasar da kada ta kara neman irin wannan bukata har sai FIFA ta sauya salon kada kuri'ar ta.

Wakilan kwamitin zartarwa na Hukumar FIFA 22 - kowanne da kuri'a daya - suka zabi Rasha domin daukar nauyin gasar ta 2018, yayin da Ingila ta samu kuri'u biyu kacal.

"A gani na bai kamata mu sake neman wata gasar ba har sai mun tabbatar cewa za a sauya tsarin da ake bi," a cewar Anson.

Ingila wacce rabonta da ta dauki bakuncin gasar tun 1966, kuma ta kasa samun gasar a shekarar 2006, an fitar da ita ne tun a zagayen farko.

'Na ka sa fahimtar abin da ya faru'

Tawagar Ingila ta yi imanin cewa shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afrika Issa Hayatou ya zabe su, tare da shugaban tawagar Geoff Thompson.

Wata majiya ta ce shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tsakiyar Amurka Jack Warner da Sakataren sa Chuck Blaze,r na daga cikin wadanda suka baiwa Ingila tabbacin za su kada mata kuri'a.

Rasha ta samu ( kuri'u 9), Spain/Portugal ( kuri'u 7), sai Holand/Belgium (kuri'u 4), daga nan sai aka tafi zagaye na biyu.

Daga nan ne kuma Rasha ta lashe da gagarumin rinjaye na kuri'u 13, inda Spain/Portugal suka samu 7, sai Holand/Belgium da suka kare da biyu.

Image caption Magoya bayan Rasha suna murnar nasar da suka samu

Duka Yarima Williams da Fira minista David Cameron da Beckham sun yi iya kokarinsu domin nemawa Ingila goyon baya, amma Anson ya ce, wakilan sun ki cika alkawarin da suka dauka inda suka zabi abokan hamayyar Ingila.

"Har yanzu na ka sa fahimtar abin da ya faru," kamar yadda ya gaya wa wani taron manema labarai a ranar Juma'a a Zurich.

"A daidai lokacin da kake da shirin da ya fi kowanne da fuskar kwarewa, rahoton tattalin arzikin mu ya fi kowanne, kuma kamar yadda mutane suka gaya mana, jawabin da muka gabatar ya fi kowanne, akwai mamaki ace duka wannan ya ta shi a banza".

"Sun mana alkawarin za su zabe mu, amma sun ce wai kafafen yada labaranmu ne suka cuce mu, gaskiya ni ban yarda ba".

Sai dai ya ki bayyana wadanda suka kasa cika alkawarin da suka dauka.

Image caption Wani mai goyan bayan Ingila na jimami bayanda kasar ta sha kayi

Gasar 2022

A daidai lokacin da aka zabi Rasha domin daukar nauyin gasar ta 2018, wani abin mamaki shi ne yadda aka zabi kasar Qatar domin ta shirya gasar a 2022 da gagarumin rinjayen kuri'u 14.

Australia wacce ta samu kyakkyawan yabo daga FIFA, an fitar da ita a zagayen farko inda ta samu kuri'a daya kacal.

Haka dai akai ta tafiya har zuwa zagaye na uku, inda a karshe Qatar, wacce a baya FIFA ta bayyana shirinta da cewa yana cike da hadari, ta samu kuri'u 14, yayin da Amurka ta samu 8.

Kuma wannan ne ya bada damar kai gasar ta cin kofin duniya zuwa yankin Gabas ta Tsakiya a karon farko.