Kotu ta tabbatar da zaben Alpha Conde na Guinea

Zababben shugabankasar Guinea Alpha Conde
Image caption Kotun kolin kasar Guinea ta tabbatar da zaben Alpha Conde a matsayin sabon shugabankasa

Kotun koli a kasar Guinea ta tabbatar da cewa jagoran 'yan adawa Alpha Conde shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Mr. Conde dai ya lashe kashi hamsin da uku cikin dari na yawan kuri'un da aka kada, yayin da tsohon Firayim ministan kasar Cellou Dalein Diallo, ya lashe kashi arba'in da bakwai.

Zaben shugaban kasar shine na farko tun bayan da kasar ta samun 'yancin kai a shekarar alif dari tara da hamsin da takwas.

Sai dai zaben ya ci karo da 'yan matsaloli da suka hada da jinkirin kai kayayyakin zabe da kuma tashe tashen hankula tsakanin magoya bayan 'yan takarar biyu.