Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Ayyukan karfi ga mai ciki

Image caption Talauci kan sa mata masu juna biyu yin ayyukan karfi

Babban bankin duniya ya bayyana talauci da cewa wani hali ne na kasancewar dan adam cikin yunwa, da rashin muhalli, idan ba shi da lafiya ba zai iya ganin likita ba.

Ba ya ga wannan akwai fargabar abinda zai faru nan gaba, ga rayuwa irinta hannu baka hannu kwarya.

A kasashe masu tasowa, musamman a wasu kasashen da ke nahiyar Afrika talauci kan sanya mata shiga wasu ayyukan karfi don neman kwabon batarwa, a wasu lokuta mata masu juna biyu ba sa iya barin wadannan ayyuka saboda talauci ko da kuwa cikin na su karami ne.

A wasu sassa na Najeriya ma, talauci ya taimaka gaya wajen kasancewar mata a fagen ayyukan karfi, a wasu lokutan mata masu juna biyu ma kan kasance cikin rukunin matan dake wadannan ayyuka na karfi.

Shirin Haifi ki yaye da BBC Hausa ya maida hankali ne kan irin ayyukan da mata masu juna biyu ke yi don kula da iyalansu da kuma kokarin da suke na neman abin sawa a bakin salati.

Haka kuma mun ji daga bakin masana a fannin kiwon lafiya irin ayyukan dake da hadari da kuma wadanda ba su da hadari ga mace mai juna biyu a kasashenmu.