An shiga rudani kan zaben Ivory Coast

Rikicin siyasa a Ivory Coast na kara kamari, bayan rudanin da aka samu kan wanda ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu, da aka gudanar ranar Lahadi.

Kotun Tsarin mulki wadda ke tantance sakamakon zabe ta ce, Laurent Gbagbo ne yayi nasara, amma jagoran 'yan adawa, Alassane Ouattara ya ce bai amince da hakan ba.

Tun da farko hukumar zaben kasar ta bayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben.

A yanzu haka Sakatare Janar na Majalsar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya nuna goyon bayansa ga Mr Ouattara.

Akwai rahotannin barkewar rikici a titunan Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar.