Soji sun rufe kan iyakokin kasar Ivory Coast

Sojoji a kasar Ivory Coast
Image caption Sojoji a kasar Ivory Coast sun rufe dukkanin iyakokin kasar yayinda ake cigaba da fuskantar zaman dar-dar a kasar.

Sojoji a kasar Ivory Coast sun rufe kan iyakokin kasar ta kasa, da ta ruwa da kuma hanyoyin shiga kasar ta jiragen sama, a dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar rudani dangane da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar lahadi.

Hakan na faruwa ne bayan da shugaban hukumar zaben kasar ya bada sanarwar ewar dan takarar jam'iyar adawa Alassane Wattara, ya kada shugaban kasar mai ci yanzu Laurent Gbagbo.

Sai dai shugaban Majalisar da zata amince da sakamakon zaben ya bayyana cewa sakamakon zaben bashi da inganci.

Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya dai ya gargadi shugabannin biyu da cewar su warware banbance banbancen dake tsakaninsu ta hanyar lumana

Kwamitin yace zai dauki dukkanin matakan da suka dace matukar aka sami matsala dangane da sakamakon zaben