Japan da Amurka na gudanar da atisayen soji

Atisayen Sojin kasasahen Japan da Amurka
Image caption Fiye da sojojin Japan dana Amurka dubu hudu ne suka shiga cikin atisayen sojin hadin gwiwa a yankin Koriya

Kasashen Japan da Amurka sun fara wani atisayen sojoji na hadin guiwa tsakaninsu

Wannan atisaye na soji dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar rudani tsakanin kasashen Koriya ta arewa da Koriya ta kudu a yankin.

Fiye da sojojin Japan dana Amurka dubu hudu ne dai suka shiga cikin atisayen na hadin guiwa

Ana gudanar da wannan atisayen sojin hadin gwiwa a wani tsibiri dake kudancin kasar Japan.