Korea ta Kudu ta yi barazanar kai hari ta sama

Ministan tsaro mai jiran gado na Korea ta kudu

Ministan tsaron kasar Koriya ta Kudu mai jiran gado ya ce kasarsa zata yi amfani da karfin da take da shi na mayakan sama, idan aka sake samun barkewar rikici da Koriya ta Arewa.

Kim Kwan- Jin ya yi wannan na bayani ne ga majalisar dokokin kasar, bayan harin da Korea ta Area ta kai a kan wani tsibiri, mallakin Korea ta Kudu a makon jiya.

Ministan tsaron Korea ta Kudu mai jiran gado ya yi wadannan kalaman ne musamman domin kwantad da hankalin 'yan kasarsa.

Gwamnatin kasar dai ta sha kakkausar suka dangane da martanin da ta mayar abun da wasu 'yan kasar suka bayyana da cewa mai rauni ne.

A waje daya kuma yayinda ake ci gaba da zaman zulumi a yankin na Koriya, kasashen Amurka da Japan na ci gaba da gudanar da wani gagarumin atisayen hadin gwiwa.