An zargi rundunar tsaro ta JTF da hallaka farar hula

Masu gwagwarmaya na Niger Delta
Image caption Masu gwagwarmaya na Niger Delta

A Nigeria, wata kungiyar kare hakin bil adama ta yi zargin cewa harin da sojin Najeriya suke kai wa yankin Nijer Delta mai azrkin man Petur yayi sanadiyyar mutuwar mutane 150.

An ambato shugaban kungiyar wadda ake kira Forum of Justice and Human Rights Defense, Mr Oghebejabor Ikim ya na cewa baya ga hallaka farar hulla a harin an kuma kona gidajen mutane da dama.

Sai dai rundunar tsaron ta JTF, a yankin Niger Delta ta musanta wanan zargi.

Rundunar jami'an tsaron ta JTF ta ce ta kai farmakin ne a wasu sansanonin uku dake kusa da garuruwan Ayakoroma da okrika a jihar Delta.

Wani babban jami'in rundunar sojojin Nigeria ya ce an kai harin ne wasu sansanoni da ke karkashin ikon John Togo.

Ana zargin John Togo da wasu aikace aikacen da suka hada da fashi da makami da fyade da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudi.