Ranar Nakasassu ta Duniya

Nakasassu
Image caption Nakasassu

Yau ce ranar tunawa da nakasassu ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazarin halin da nakasassun ke ciki a kasashen duniya.

A wannan rana akan yi kokarin jan hankalin hukumomi game da muhimmacin bayar da cikakkiyar dama, da 'yanci ga nakasassun ta fannonin zamantakewa, da siyasa, da tattalin arziki da sauran abubuwan da suka shafi ci gaban rayuwarsu.

Nakasassun dai sun dade suna fama da manyan matsaloli a kasashe da dama musamman masu tasowa da galibi talauci da rashin aikin yi ya dabaibaye su.