Wikileaks ya ce daga sama ne aka hana Google aiki a Sin

Bayanan sirri na baya- baya da shafin yanar gizo na Wikileaks ya bankado game da diplomasiyyar Amurka, na nuni da cewa matakin da Kasar Sin ta dauka akan shafin yanar Gizo na Google, ya samo tushe ne daga sama.

Bayanan na bayyana irin shakkar da shugabannin kasar Sin ke da ita akan abubuwan da aka wallafa a yanar gizo, da kuma irin zargin da ake mata na taka rawa wajen satar shiga shafukan Google ba tare da izini ba, lamarin da har ya janyo shafin na Google ya daina aiki a kasar Sin.

Wani babban mai fada a ji a kasar ya shaidawa ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beijin cewa wannan wani mataki ne da suka dauka, wanda kuma babu abinda ya janyo haka sai tsantsar siyasa.

Jami'an diplomasiyyar Amurka dai sun bayyana cewa ba a bayyane take ba ko shin manyan shugabannin Sin kamar shugaban kasar da Prime Ministan sun san da wannan batu ba.

Sai dai kamar yanda bayanin da aka bankado din ke nunawa, wani babban dan siyasar kasar ya nuna matukar kiyayyarsa ne ga shafin yanar gizo na gooogle din bayan da ya shiga ciki ya taradda wasu kalamai da suke kalubalantar sa.

Sannan kuma bayanan sun nuna cewa Jami'an Sin sun shaidawa gwamnatin Amurka kan ta rage ingancin hotunan da shafin yanar gizo na Google din ke nunawa akan sojin Sin da ma wadansu wurare.