Kasar Ivory Coast ta fada cikin rudani

Shugaba Laurent Gbagbo
Image caption Shugaba Laurent Gbagbo

A Ivory Coast an gudanar da bikin rantsar da shugaba Laurent Gbagbo a matsayin shugaban kasar na gaba, bayan ya kwashe shekaru goman da suka gabata a kan karagar mulki.

Laurent Gbagbo ya yi biris da matsayin kasashen duniya, cewa a zahiri dan takarar adawa, Alassane Ouattara, ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanan nan.

Firayim ministan kasar, wanda ya ce ya amince da Alassane Ouattara a matsayin sabon shugaban kasar, ya mika takardar yin murabus.

Magoya bayan Shugaba Gbagbo tare da abokan kawancensa ne dai suka hallara a fadar shugaban kasar wadda ke tsakiyar birnin Abidjan domin rantsar da shi a wani wa'adi na tsawon shekaru biyar.

To amma rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke da dukkanin sakamakon da ya fito daga rumfunan zabe dubu ashirin na kasar, ta ce a bisa duk wata raskwana da ta yi, Mr Ouattara ne ya lashe zaben.

Tuni dai Mista Ouattara ya samu goyon bayan kasashen duniya, haka kuma a cikin gidan ma, ya samu goyon bayan kungiyar yan tawaye.

Shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, Victor Gbeho, ya ce shugabannin kasashen kungiyar za su yi taron gaggawa a Abuja da safiyar ranar Talata mai zuwa, domin ganin irin martanin da za su mayar ga lamarin.

Mista Gbagbo dai na da goyon bayan manya-manyan kusoshin rundunar sojojin kasar da kuma ma'aikatun tsaro akalla dai har zuwa daren Juma'a.

An rufe kan iyakokin kasar sannan an toshe dukkanin wasu kafofin yada labarai na kasashen waje, yayin da kuma gidan talabijin na kasar ke hannun Mr Gbagbo.

Rahotanni sun ce magoya bayan Alassane Ouattara ma suna shirye-shiryen gudanar da nasu bikin nan gaba a yau, domin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar ta Ivory Coast.

Dakarun kiyaye zaman lafiyar majalisar dinkin duniya ne zasu tabbatar da tsaro a lokacin bikin.

Hakan na nufin Cote d'Ivoire din za ta sami shugabanni biyu kenan.

A daren jiya dai an bayar da rahotanni na zanga zanga a cikin birnin da kuma wadansu sauran birane na kasar.

Shi dai wannan zabe da aka gudanar na cikin zabubbukan da suka fi tsada matuka a duniya; an kuma shirya shi ne da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan siyasa da yakin basasar da aka shafe shekaru goma ana fama da su.

To amma a yanzu rudamin da ake cikim na barazanar tsunduma kasar cikin wani rudanin daban.