An rantsar da shugabanni biyu a Ivory Coast

rikicin Ivory Coast
Image caption rikici a Ivory Coast

Ana cikin rudani a Ivory Coast bayanda aka rantsar da mutane biyu a matsayin shugaban kasa, sanadiyyar zaben ranar Lahadin da ta wuce.

An fara ne da bikin rantsar da shugaba Laurent Gbagbo mai shekaru goma bisa mulki, wanda abokin hamayyarsa Alassan Ouattara, da hukumar zaben kasar, da majalisar dinkin duniya, da sauran kasashen duniya ke musanta nasarar da yake ikirarin ya yi a zaben.

A lokacin rantsuwar, Mr. Gbagbo ya yi Allah wadai da abinda ya kira, tsoma baki na kasashen waje.

Bayan sa'o'i kadan kuma sai aka rantsar da Mr. Outtara a wani bangaren dabam na babban birinin kasar.

Wakilin BBC ya ce an gudanar da zaben ne domin kawo daidaito da zaman lafiya bayan yakin basasar da aka kwashe shekaru goma ana yi, sai dai zaben na neman zama ummul haba'isin wani sabon rikicin a kasar da yanzu ta ke da shugabanni guda biyu.

Kasashen duniya dai na cigaba da kira ga Laurent Gbagbo da ya sauka daga kan mulki.

Gamayyar kasashen Afrika ta ce za ta dau mataki kan duk wadanda ke yiwa sakamakon zaben Ivory Coast kafar ungulu.

Haka kuma asusun lamuni na duniya IMF ya ce zai yi aiki ne kawai da gwamnatin da majalisar dinkin duniya ta amince da ita.

Tuni dai sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon ya nemi Mr. Gbagbo da ya mika mulki ga wanda ya yi nasara a zaben.