Arangama tsakanin soji da yan Boko Haram a Najeriya

Boko Haram
Image caption gawarwakin Boko Haram

A jihar Borno da ke Najeriya, ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Ahlus Sunnah wal Jihad ne da aka fi sani da Boko Haram.

An dai ba da rahoton jin karar bindigogi a Maiduguri, babban birnin jihar a unguwannin Budum zuwa Kofa Biyu zuwa state low Cost, inda a baya aka bayyana cewa nan ne tushen rikicin Boko Haram.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Jihar Borno, ya tabbatarwa da BBC faruwar al'amarin amma ya ce sai ya ganewa idonsa abin da ke faruwa zai yi karin bayani.

A 'yan watannin da suka gabata dai wadansu mutanen da ake zargin 'yan Boko Haram din ne sun hallaka mutane da dama a birnin na Maiduguri da ma wasu sassa na arewacin Najeriya.