Thabo Mbeki na shawarwari a Cote D'voire

Thabo Mbeki
Image caption Tsohon Shugaban Africa ta Kudu

Tsohon shugaban Afurka ta Kudu Thabo Mbeki yayi ganawa a karo daban daban a kasar Cote D'voire da mutane biyun da kowanne ke ikirarin shi ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Thabo Mbeki ya fara ganawa da shugaba Laurent Gbagbo a fadar gwamnati, kafin daga bisani ya gana da abokin hamayyar Mr Gbagbon, watau Alassane Ouattara, a Otel din da dakarun tsaron Majalisar Dinkin Duniya ke gadinsa.

Kungiyar tarayyar Afrika ce ta tura Mr Mbeki domin ya laluba hanyar warware takaddamar cikin lumana.

Da alama abu na farko da Mr Mbeki zai fi baiwa fifiko shine yayi kokarin rarrashin dakarun 'yan tawaye, wadanda ke iko da yankin arewacin kasar tun bayan da aka fara yakin basasa a shekara ta 2002, da su kwantar da hankalinsu a yayin da yake kokarin nemo bakin zaren.