JTF ta amsa cewa mai yuwa an hallaka farar hulla

Masu gwagwarmaya

Wani kakakin sojan Nijeriya ya ce mai yuwa akwai fararen hular da aka kashe a lokacin wani samame da aka kai a kokarin kama jagoran wata kungiyar 'yan bindiga a yankin Niger Delta.

Kakakin rundunar hadin guiwa ta JTF a yankin Niger Delta, Laftanar Kanar Timothy Antigha ya shaidawa BBC cewa watakila akwai fararen hular da aka rutsa da su a gumurzun da aka yi ranar Laraba a kauyen Ayakoromor.

Wani mai fafutukar kare hakkin jama'a wanda ya kai ziyara kauyen da abun ya faru ya ce yana kokarin tantance rahotannin dake nuna cewar an kashe mutane tara.

Sai dai wata kungiyar kare hakkin dan adam din na cewa mutane akalla sha takwas ne suka mutu.

Tun farko wata kungiya daban ta yi ikrarin cewar an hallaka mutane 150, rahoton da kakakin rundunar hadin guiwa ta JTF ya karyata.