Shara ta zama matsala a garin Kauna dake Nijar

A Jamhuriyar Nijar a garin Kauna dake Jihar Maradi matsala yawan shara ce ke ciwa mutanen garin tuwo a kwarya.

Matsalar dai itace duk da yake akwai ma'aikatar magajin gari a garin, wannan matsala ta shara na damun mazauna garin.

Sai dai kuma su Mazauna garin na danganta wannan matsala da rashin biyaya da ake cewa suna yi wa magabatansu, lamarin da ya sa mahukunta ke nuna halin ko in kula ga wannan gari.

Sai dai kuma ma'aikatar magajin gari ta bayyana cewa ba ta da kudi saboda mutanen garin basa biyan haraji.