Shafin Wikileaks ya sake bankado wani sirrin

A wani bayani da shafin yanar gizo na Wikileaks ya bankado game da Amurka, bayanai na nuni da wadansu jerin mahimman abubuwa da Amurka ke dauka da matukar mahimmanci idan ana batun harkar tsaron cikin gida.

Bayanan dai sun fassara yanda Amurka ke daukar sha'anin tsaron ta na cikin gida.

Baya ga wadansu abubuwa da suka shafi harkar sadarwa, da bututan iskar gas, ciki har da hakar ma'adanai a Kasar Congo, da wani kamfani mallakin Kasar Australia, da ma kuma wani na Kasar Denmark.

A watan Fabrairun bara ne dai Amurka ta aike da sako ga jami'an ta dake kasashen waje, inda ta umarce su da su jera mata sunayen duk wadansu abubuwa da ka iya shafar lafiyar al'ummar ta ko tattalin arzikin ta, ko harkar tsaron cikin gida na Amurka.

A Birtaniya jerin sunayen sun hada da wasu wurare kama daga Cornwall ya zuwa Scotland, ciki har da bayanai akan harkar sadarwa, da inda aka girke duk wasu keburan cibiyoyin hanyoyin sadarwa da suka tsallaka zuwa wadansu kasashe.

Wadansu daga cikin kamfanonin dake da hannu a kera makamai na cikin jerin da aka aikewa Amurkan, ciki har da wani kamfani da ya shahara a aiyukan cikin teku da ke Edinburgh, wanda bayanan suka rawaito cewa ya yi suna wajen yin aiyukan karkashin teku da suka danganci makamin nukiliya.