Tawagar Mista Gbagbo ta ziyarci shugaban Ghana

Laurent Gbagbo
Image caption Taron ECOWAS zai shata ma Kot Dibuwar makoma

Shugaban kasar Kot Dibuwa, Laurent Gbagbo, ya tura wata tawaga zuwa kasar Ghana, a daidai lokacin da siyasar kasar ta sarke.

Hakan ya biyo bayan ayyana kansu a matsayin shugabannin kasar da ‘yan takarar shugabancin kasar guda biyu suka yi.

Tawagar ta ce manufarta ita ce ta bayyana wa shugaba John Atta Mills halin da ake ciki a kasar ta Kot Dibuwa.

Sai dai ga alama Mista Laurent Gbagbo yana neman goyon bayan shugaban kasar ta Ghana ne, gabannin taron gaggawar da Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afrika, ECOWAS za ta gudanar a birnin Abujar Nigeria a gobe don duba lamarin.

Shugaban kasashen duniya, ciki har na Faransa, tsohuwar uwar gijiyar mulkin mallakar kasar, suna kira ne ga Shugaba Gbagbon day a ba da kai a kan cewa an kada shi a zaben.