Iran na ganawa da kasashen duniya

Tashar nukiliya ta Bushehr da ke Iran
Image caption Wannan shiri ya dade yana haifar da cece-kuce tsakanin Iran da kasashen Yamma

Kasar Iran na tattaunawa da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyarta da ke ci gaba da jawo cece-kuce a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Wannan ne karo na farko da ake yin irin wannan taro a cikin sama da shekara guda, sai dai masu sharhi na ganin zai yi wuya a samu wani ci gaba.

A ranar Lahadi Iran ta ce ta samar da makamashin Uranium a cikin gida wanda zai ba ta damar sarrafa shi. Amurka dai ta yi Allah wadai da matakin, amma Tehran ta ce a yanzu za ta halarci taron da "kwarin giwa".

Da yake magana a gidan talabijin na kasar, jagoran shirin nukiliyar Iran Ali Akbar Salehi, ya ce taron na Geneva zai amfani sauran kasashe ne kawai, amma ba wai Iran ba.

Amurka da kawayenta sun yi amannar cewa Iran na kokarin kyara makaman nukiliya ne, amma kasar ta nace cewa shirin na ta na zaman lafiya ne.

Mai shiga tsakani na Iran kan harkokin nukiliya Saeed Jalili, na gana wa da jami'ar hulda da kasashen waje ta Tarayyar Turai Catherine Ashton, da manyan jami'an kasashe biyar masu kujerar naki a Majalisar Dinkin Duniya.

Wadannan kasashe dai su ne Amurka da Rasha da China da Faransa da Burtaniya - hadi da kuma Jamus.