Bom ya kashe mutane 40 a Pakistan

Bom ya kashe mutane 40 a Pakistan
Image caption Wannan ne hari na baya-bayan nan da aka kai a yankin

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Arewa maso Yammacin Pakistan ya hallaka mutane 40, kamar yadda jami'an yankin suka bayyana.

An kai harin ne a wani ginin gwamnati da ke cibiyar Mohmand a daidai lokacin da jami'ai ke tattauna wa da kungiyoyin da ke adawa da Taliban.

Wasu daruruwan mutane kuma sun samu rauni, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

Yankin wanda ke makwaftaka da kasar Afghanistan, matattarar 'yan Taliban da al-Qaeda ne. Kuma an sha kai hare-hare a wurin.

An debe wadanda suka jikkata

Fiye da mutane 100 ne ake kyautata zaton suna cikin ginin, inda ake tattauna wa tsakanin jami'an gwamnati da kungiyoyin kabilu da kuma masu adawa da Taliban.

Daya daga cikin jami'an Mohammad Khalid Khan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, shugabannin kabilu da 'yan sanda na cikin wadanda suka rasu a harin.

An garzaya da kusan mutane 25 daga cikin wadanda suka jikkata zuwa Peshawar domin yi musu magani.

Daya daga cikin mutanen da aka hara, shugaban siyasar Mohmand Amjad Ali Khan, ya tsallake rijiya da baya.