Majalisar Dinkin Duniya ta fara janye ma'aikatanta daga Ivory Coast

Majalisar Dinkin Duniya ta fara janye ma'aikatanta da ba a matukar bukatar ayyukansu daga Ivory Coast zuwa makwabciyar kasar Gambia.

Mai magana da yawun majalisar dinkin duniya Martin Nesirky ya bayyana cewa kimanin ma'aikata dari hudu da sittin ne za'a janye zuwa makwabciyar kasa Gambia na dan wani lokaci domin su ci gaba da aiki daga can.

Ya dai bayyana cewa sauran kuma zasu ci gaba da ayyukan nasu ne a kasar ta Ivory Coast.

Majalisar dinkin duniya dai na da dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin dubu goma a kasar, wanda nauyin tabbatar da hakikanin sakamakon zaben shugabancin kasar da aka yi a kwanan nan ya hau kansu.

Wanda kuma rahotonsu ke bayyana cewa Laurent Gbagbo ya sha kaye.

Sai dai kuma shi Mr. Gbagbo din ya ki amincewa ya sauka daga kan mulki.

Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya sun amince ne da nasarar dan takara karkashin tutar adawa Alassane Quattara a matsayin shugaban kasar.

Tashin hankali dai na ci gaba da zafafa a kasar, tun bayan da 'yan takarar shugabancin kasar biyu suka ayyana kansu a matsayin shugaban kasa.

Sannan kuma wani mai bashi shawara ya yi gargadin korar masu wakiltar majalisar dinkin duniya a kasar.

To sai dai Mr. Nesirky ya ce an dai kwashe ma'aikatan ne a saboda rauni ta fuskar tsaro, ba wai don wannan barazanar da suka yi ba.