Kotu ta hana Shugaban Wikileaks beli

Image caption Mista Assange a lokacin da zai shiga kotu

Mutumin da ya kirkiro shafin yanar gizon nan na Wikileaks wanda ya wallafa bayanan sirrin da ya fusata Amurka tare da bata kunya, Julian Assange, ya ce ba zai bari a tasa keyarsa zuwa kasar Sweden ba.

Wata Kotu a Ingila ta hana Mista Assange wanda dan asalin kasar Australia ne beli, bayan ya musanta zargin fyade da ake masa a kasar Sweden.

Julian Assange, ya mika kansa ga 'yan sanda a Landan. An kama shi ne a madadin mahukuntan kasar Sweden bisa zargin fyade da ake masa, lamarin da ya musanta.

Kotun dai ta bukaci jami'an tsaro da su rike Mista Assage har zuwa mako mai zuwa kafin ta kara zama.

Mista Assange ya shaidawa alkalin kotun Majistare da ke Westminster cewa zai kalubalanci tasa keyarsa zuwa Sweden da mahukuntan kasar ke bukata.

Mai magana da yawun Mista Assange ya ce kama shi da aka yi wani hari ne a kan yancin 'yan jaridu.

Kristinn Hrafnsson ya ce, shafin Wikileaks ba zai daina wallafa bayanan sirri ba; "Kama Mista Julian Assange ba zai hana shafin wallafa bayanan sirri ba, kuma nan ba da dadewa ba zamu kara wallafa wasu bayanan."