ECOWAS ta dakatar da Ivory Coast

Image caption Tambarin kungiyar Ecowas

Shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ko CEDEAO sun dakatar da kasar Ivory Coast saboda da rikicin shugabanci da kasar ta shiga.

Shugabannin wanda suka gudanar da taro a babban birnin Najeriya, Abuja sun tabbatar da Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya wanda ya bayyana matsayin kungiyar bayan sun kammala taron ya bukaci shugaba Laurent Gbagbo da ya yi murabus.

A yanzu dai duka mutanen biyu, wato Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara sun fara yunkurin kafa gwamnati.

Majalisar dinkin duniya da kasar Faransa da Tarayyar Afrika sun yi kira ga Mista Gbagbo da yayi murabus, amma kawo yanzu bai nuna alamar yin hakan ba.

Karanci da Tsadar Abinci

Bayanai sun nuna cewa a yanzu ana fama da karancin kayan masarufi a kasar Ivory Coast, yayinda farashin wasu kayayyakin ciki har da Cocoa ya tashi, yayin da ake ci gaba da fama da kiki-kakan siyasa.

Shaguna da dama sun rufe saboda karancin kayayyaki da suka hadar da nama, kifi, fetur, iskar gas din girki da sauransu.

Kasar ivory Coast dai ita ce kasar da ta fi kowacce samar da Cocoa a duniya.

Yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar, majalisar dinkin duniya ta fara janye ma'aikatanta da aikinsu bai zama dole ba daga kasar.

A ranar Litinin mai shiga tsakani na tarayyar turai, tsohon shugaban Afrika ta Kudu Thabo Mbeki ya bar kasar ta Ivory Coast bayan tattaunawar da ya gudanar da bangarorin biyu ya kasa kawo karshen rikicin.

Kasar ta Ivory Coast dai ta rabu biyu tun shekarar 2002 sakamakon yakin basasa.

A baya dai ana ganin kasar a matsayin watta aljannar zaman lafiya a yammacin Afrika.

Zaben shugabancin kasar na bana dai ya zo a karshen tattaunawar zaman lafiyar da aka yi tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.